Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Adamawa Fatima Atiku ta ce har yanzu dai wannan majinyacin da aka sace wa koda Isa Hamman na amfani da na’uran da ke taimaka wa mutum ya rayu wato (lifesaving machine) a asibitin koyarwa na Aminu Kano bai mutu ba.
Ta yi bayanin cewa idan ba a manta ba a shekarar 2016 ne wani likitan fida a wata asibitin da ke zaman kanta ya sace wa Isa koda wanda hakan ya zama dole ya yi amfani da na’uran domin rashin samun kodan da zai yi daidai da jikinsa.
Ta ya bayanin cewa lokacin da aka kawo majinyacin asibitin Aminu Kano, asibitin ta yi kokarin nema masa koda daga wajen ‘yan uwan sa amma hakan bai yiwu ba saboda bayan gwaje gwajen da asibitin ta yi ta gano cewa ‘yan uwan nasa ba za su iya taimaka masa da kodarsu ba saboda suma suna bukatar tasu.
A halin da ake ciki wani dan uwan Isa Hamman daga dangin mahaifinsa mai suna Umaru ya ce dan uwan sa ya yi watanni 9 kenan akan wannan na’ura taimakawa mutum domin ya rayu.
Ya kuma kara da cewa a yanzu haka sun bar asibitin Aminu Kano zuwa asibitin tarayya na jihar Gombe domin yajin aikin da likitoci ke yi sannan jikin dan uwansa babu sauki har yanzu.
Har yanzu dai ana neman kodar da za ta dace da jikin Isa Hamman.