Dole Hameed Ali ya bayyana a gaban mu ranar Laraba sanye da kayan Kwastam – Inji Majalisar Dattijai

0

Majalisar Dattijai ta ce dole ne shugaban hukumar Kwastam ta Kasa Hameed Ali ya bayyana a gabanta ranar Laraba duk da neman daga masa kafa da ya nemi majalisar tayi masa.

Majalisar tace babu abinda ya dame ta da taron da yace zai hana shi amsa kiran nasu.

Majalisar ta ce dole ya bayyana gobe kuma cikin Unifom din kwastam.

Shugaban hukumar kwastam Hameed ta kasa Ali ya rubuta wa majalisar dattijai wasika cewa ba zai samu damar bayyana a gaban majalisar ranar Laraba ba saboda wani taro da zai halarta.

Majalisar dattijai sun nemi Hameed Ali ya bayyana a gaban ta domin yi musu bayanai akan wasu abubuwa da ya shafi hukumar.

Majalisar ta ce idan zai bayyana a gabanta ya tabbata ya saka unifom din hukumar kwastam din.

Ko da yake Hameed Ali ya kalubalanci majalisar Kan wait sai ya saka unifom cewa kamata ya yi majalisar ta duba irin aikin da yakeyi ne ba maganar saka Unifom ba.

Yau ne a zaman majalisar akawun majalisar ya karanta wasikar Hameed Ali din.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Ahmed Lawan ya ce basu gamsu da wannan dama da Hameed Ali ya nema ba.

Share.

game da Author