Wasu Fulani makiyaya sun kai hari kauyen Tombo-Mbalagh na karamar hukumar Buruku dake jihar Benue.
Mai anguwan kauyen Justina Sorkaa ta ce a makon da ya gabata makiyaya sun kashe mutane 8 sannan wasu mutane 3 sun bace a kauyen.
Kwamishinan rundunan ‘yan sandan jihar Bashir Makama ya tabbatar da mutuwar mutane 6.
Bayan haka gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ce ya ba Fulani makiyayan kwanaki 2 da su tattara inasu-inasu su bar kauyen.
Gwamnan jihar ya ce a shekarar 2015 mutanen jihar suka amince da wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu da makiyayan a jihar wanda hakan ya hana su ajiye makamai kuma suka kasa kare kansu lokacin da makiyayan suka far musu.
Ortom yace domin tabbatar da cewa makiyayan sun bar kauyen da kuma samun zaman lafiya a kauyen zai turo jami’an tsaron domin su raka su ficewa daga garin.