Shugaban Hukumar Kwastam na Kasa Hameed Ali ya gana da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki a ofishinsa bayan kin aamincewa da majalisar tayi na dole sai ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tambayoyi.
Hameed Ali da Saraki sunyi ganawan ne a asirce da yamman Laraba.
Duk da cewa an sami sabani tsakanin majalisar da shugaban hukumar kwastam din wasu bayanai sun nuna cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya baki akan cecekucen inda ya yi kira ga bangarorin biyu da su sasanta kansu domin guje ma yawan sabani da ake samu tsakin majalisar da bangaren zartaswa.
Shugaban hukumar kwastam Hameed ta kasa Ali ya rubuta wa majalisar dattijai wasika cewa ba zai samu damar bayyana a gaban majalisar ranar Laraba ba saboda wani taro da zai halarta.
Majalisar dattijai sun nemi Hameed Ali ya bayyana a gaban ta domin yi musu bayanai akan wasu abubuwa da ya shafi hukumar.
Majalisar ta ce idan zai bayyana a gabanta ya tabbata ya saka unifom din hukumar kwastam din.
Yau ne a zaman majalisar akawun majalisar ya karanta wasikar Hameed Ali din.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Ahmed Lawan ya ce basu gamsu da wannan dama da Hameed Ali ya nema ba.
A dalilin haka majalisar ta ce dole ne shugaban hukumar Kwastam ta Kasa Hameed Ali ya bayyana a gabanta ranar Laraba duk da neman daga masa kafa da ya nemi majalisar tayi masa.
Bayan tattaunawa da Ali yayi da shugaban majalisar dattijai da yamman yau, ya amince ya amsa gaiyatar majalisar gobe Laraba.
Abin tambaya shine, shin zai zo sanye da kayan Kwastam din ne ko a’a?