Buhari zai rubuta wa majalisar dattijai wasika domin sanar musu da dawowarsa aiki ranar litini

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mika wa majalisar Kasa wasikar sanar dasu dawowa aiki bayan hutu da ya dawo daga kasar Ingila.

Maiba shugaban kasa shawara akan harkar yada labarai Femi Aesina ne ya sanar da haka a shafinsa na twitter.
Yace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai mika wasikar sanar da majalisar dattijai dawowa aikinsa ranar litini mai zuwa.

Bayan haka kuma ya musanta rade-radin da ake ta yadawa wai mataimakinsa Yemi Osinbajo zai cigaba da rike kasar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika godiyarsa ga ‘yan Najeriya kan addu’o’i da suka yi ta yi masa tun da ya bar kasa zuwa kasar Ingila domin duba lafiyarsa.

Buhari ya fadi hakanne a lokacin da ya ganawa da jami’an gwamnati a fadar shugaban kasa jim kadan bayan ya dawo daga kasar Ingila.

‘’Na gode da addu’o’in da Musulmai da Kiristoci su ka yi ta yi mini.

‘’Hakan ya nuna cewa duk da wahalhalun da kasa Najeriya ta ke fama da shi mutanen Najeriya tare da gwamnati kai da kafa.

Buhari ya kara da cewa ya sami sami sauki sosai domin irin kulan da likitoci suka bashi a tsawon zaman sa a kasar Ingila.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yace mutanen Najeriya da su jami’an gwamnati sun yi mutukar murna yadda suka nuna farin cikinsu da dawowar shugaban kasan.

Ya kuma yabi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yadda ya girmama tsarin mulkin kasa inda da ya sakar mai ragamar kulkin kasa a lokacin da ba ya kasa har zuwa yanzu da ya dawo.

Daga karshe shugaban kungiyan gwamnonin Najeriya Abdulaziz Yari, ministan yada labarai Lai Muhammed, shugaban jami’an tsaro Abayomi Gabriel Olonishakin suma sun yi nasu tsokacin dawowar shugaban kasan.

Shugaban kasa Buhari ya dawo kasa Najeriya daga kasar Landan bayan kwanaki 51 da yayi yan ganin likitoci.

Share.

game da Author