Sakon Buhari ga ‘yan Najeriya

0

Kamar yadda muka samu daga shafin mai taimakawa Shugaban kasa kan sababbin kafafen yada labarai Bashir Ahmed, shugaba Buhari ya godewa ‘yan Najeriya musamman addu’o’i da akayi ta yi masa domin samun lafiya.

Ga sakon

Ina matukar godiya ga dukkan ‘yan Nigeria – Musulmai da Kirista wadanda suka yi min addu’o’i kuma suke ci gaba da yi min akan rashin lafiya ta. Hakan ya nuna cewa duk da irin wahalhalun da aka fama da su na tattalin arziki, har yanzu ‘yan Nigeria suna tare da goyon bayan wannan gwamnatin ta mu wajen kawo karshen wadannan matsaloli.

Babban hanyar da zan bi na saka muku shi ne na sake sadaukar da kaina wajen yi muku aiki, kare martabar ku da kuma rike amanar da kuka danka mana. Ina godiya kwarai da gaske.

Yanzu na ji sauki sosai, duk da akwai yiwuwar cikin satittuka masu zuwa zan iya sake komawa don sake duba lafiyar tawa.

Maimakon aiko tawaga bisa tawaga zuwa Abuja don taya ni murnar dawowa, zan so nayi kira gare ku da ku zauna ku ci gaba da yi wa kasar mu addu’ar zaman lafiya, hadin kai, ci gaba da bunkasa.

Share.

game da Author