Buhari ya kira Obasanjo da Gwamnan Kogi

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kira tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga kasar Ingila domin tayi shi murnan zagayowar ranar haihuwarsa yau.

An gudanar da bukin zagayowar ranar haihuwar Obasanjo yau a garin Abeokuta da kaddamar wata sabuwar dakin karatu da ya gina.

Buhari ya yabi Obasanjo kan irin shugabanci nagari da yayi musu a lokacin da suke aiki soji.

Bayan haka Buhari ya kira gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

Buhari yayi masa fatan alkhairi sannan ya ce masa lallai yana samun sauki kuma ya kusa dawo wa kasa Najeriya domin ci gaba da aiki.

Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo bai yi kasa kasa ba wajen yaba ma Buhari da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya.

Obasanjo yace shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai bashi kunya ba tun da ga ranar da ya hau kujeran mulkin kasa Najeriya har zuwa yanzu.

Obasanjo yace a sanin Buhari da yayi tuntuni ba mutum bane da yake da amsoshi sosai ga yadda za’a bunkasa tattalin arzikin kasa, amma yayi matukar canzawa yanzu domin ana ta samun nasarori akan hakan a kasa Najeriya.

Ya ce dole a yabi Buhari saboda nasarorin da ya samu musamman na yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.

Ya kara da cewa Buhari yayi abin azo a gani a tsaon kwanakin da yayi yana shugabancin kasa Najeriya.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da mara masa baya domin samun nasara akan abinda ya sa a gaba na gyaran Najeriya.

Share.

game da Author