Jiragen saman kasashen waje basu amince da su yi amfani da filin jirgin saman Kaduna ba a madadin na Abuja da za’a kulle.
Jirgin sama na Ethopian Airlines ne kawai ta yarda ta yi amfani da filin jirgin saman Kaduna din.
Gwamnatin tarayya ta sanar da rufe filin jirgin saman Abuja daga karfe 12 na safiya Laraba zuwa 9 ga watan Afirulu.
Duk da cewa wadansu masana sun nuna rashin amincewarsu da dawo da ayyukan tafiye tafiyen jiragen sama zuwa Kaduna gwamnati ta ce Kadunan ne zatayi amfani da shi.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ziyarci filin jirgin saman Kaduna a karshen makon nan inda ya duba matsayin aikin da akeyi a filin.
Ministan sufirin jiragen saman Najeriya Hadi Sirika yace gwamnatin ta gama shiri domin fara jigilan matafiya daga filin ta Kaduna.