Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta doke Enyimba da ci 3 da 1 a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.
Plateau United ta buga kunnin doki da Shooting Stars a garin Ibadan.
Kungiyoyin kwallon kafa na Katsina United, Gombe United, Elkanemi na Barno da Nasarawa United duk sun sha kayi a wannan mako
Ga yadda ta kaya a wasannin.
Rivers United FC 1-0 Rangers International FC
FC IfeanyiUbah 2-2 Abia Warriors FC
MFM FC 1-0 Remo Stars FC
Niger Tornadoes FC 2-0 Nasarawa United FC
Akwa United FC 1-0 El-Kanemi Warriors FC
Lobi Stars FC 1-0 Gombe United FC
Sunshine Stars FC 1-0 Wikki Tourists FC
ABS FC 1-0 Katsina United FC