Bin hanyar Abuja – Bwari- zuwa Kaduna hadari ne yanzu, matafiya a kula

0

Ganin cewa matafiya sun koma bin babban hanyar Abuja zuwa Kaduna ta Zuba saboda tsaro da gwamnati ta samar a dalilin rufe filin jirgin saman Abuja, hanyar ta Bwari ya zama tashan ‘yan fashi da makamai.

Wannan himma da gwamnati tayi yayi wa matafiya dadi musamman ganin yadda tsaro ya kankama a hanyar saida ana tuya ne amma an manta da albasa domin hanyar Abuja zuwa Kaduna ta Bwari yanzu ya zama hanyar bi da alwalanka.

Bayan sace mutane da akeyi barayi na sata kamar babu gobe a hanyar.

Mun tattauna da wadansu wanda barayi sukayi garkuwa dasu a makon da ya gabata kuma Allah ya kwace su da kyar.

“ Mun fito daga garin Abuja da kamar Karfe 6:30 na yamma, bayan takaddama da mukayi da direban motar da muka shiga cewa abi ta Zuba wasu daga cikin motar kuma suna cewa sunfi so a bi ta hanyar Bwari domin tafi sauri.

“Bayan munyi tafiyar kilomita 48 kwatsam sai muka ga dandazon mutane da motoci gab da daidai ma’aikatar hanya na SCC.

“Mun tsaya a daidai motar mu kuma ta samu matsala. Da muka tambaya sai aka ce mana wai barayi ne ke sata a hanyar.

“Bayan mun dan tsaya zuwa wani lokaci sai kuma aka dunguma aka ci gaba da tafiya.

“Duk da cewa ba a samu tabbacin cewa ko barayin sun tafi ba duk da haka wasun mu da suka fara tafiya sun fada cikin su.

“Da muka isa wajen bayan mun dan kara tsayawa mun taradda motoci da kayayyakin mutane watse a kan titi da wadansu a kwankwance.

“Bamu samu daman tsayawa ba sabo da hadarin dake tattare da hakan amma a gaskiya abin ya shafi mutane da dama.

Kamar yadda wadansu matafiya suka gaya mana sun ce fashi da makami ya zama sana’a a hanyar domin kusan kullum sai anyi hakan.

Kira ga matafiya da su hakura da bin wannan hanya da daddare sannan ana rokon jami’an tsaro da su gaggauta samar da tsaro a hanyar kamar yadda sukayi a babban titin Abuja zuwa Kaduna.

Share.

game da Author