Sakataren gwamnatin tarayya David Babachir ya amince ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai domin amsa tambayoyi akan kwangilar cire ciyawa da ake ta cece-kuce akai.
Sakataren gwamnatin tarayyar yace ba zai halarci zaman kwamitin majalisar dattijai wanda ta umurce shi da ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi akan korafin da akeyi kan badakalar kwangilar cire ciyawa a jihar Yobe.
Yanzu dai ya amince ya bayyana a gaban kwamitin Sanata Shehu sani domin kare kansa.
Ita ma kamfanin Rholavision Ltd wanda itace ta yi aikin cire ciyawar ta ce shugaban ta ba zai samu daman zuwa majalisar ba saboda baya nan.
Babachir ya karyata sakamakon binciken kwamitin na farko inda yace kwamitin bata gaiyace shi ba domin yayi bayani akan abinda ya faru sannan ta yi masa karya akan laifukkan da suke zargin sa yayi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi watsi da kiran da kwamitin tayi na ya sauke Babachir daga kujeransa saboda bai gamsu da bayanan majalisar ba akan wadannan laifuffuka da suke zargin Babachir ba.