Shugaban jam’iyyar PDP Ali Modu Sheriff ya ziyarci tsohon Shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar Tony Annenih a gidansa dake Abuja.
Da yake ganawa da manema labarai bayan ganawar su yace ya ziyarci Annenih domin ya nemi shawaransa akan rikicin da yake neman ya hadiye jam’iyyar.
Ya ce sun tattauna akan rikicin jam’iyyar sannan kuma ya nemi shawaransa akan yadda zasu shawo kan rikicin.
Kotun daukaka kara dake jihar Ribas ta tabbatarwa Ali Modu Sheriff da halarcin jagorancin jam’iyyar a wata hukunci da ta yanke a makon da ya gabanta.
Ko da yake magoya bayan jam’iyyar na bangaren tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Makarfi sun nuna rashin jin dadinsu akan hakan inda suka daukaka kara zuwa kotun koli.
Ali Modu ya ce zai fara aiki ranar Litini ko Talata a ofishin jam’iyyar dake Abuja.