Ana fadin karerayi akan rikicin kudancin Kaduna -Inji Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna

0

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Agyole Abeh ya gargadi mazauna kudancin Kaduna da su daina yin amfani da rikicin da ake ta fama da shi a yankin domin son zuciya.

Kwamishinan yace wasu abubuwan ana rurutasu ne domin son zuciya amma ba wai gaskiyar abin da ya faru bane ake fadi.

Ya ce abinda suka gano a yankin shine rikicin yana faruwa ne a sanadiyyar daukan fansa da mazauna garuruwan yankin suke yi tsakaninsu da fulani.

Ya yi kira ga mazauna yankin da su daina amfani da hakan domin sanar da mutane karerayi akan abubuwan da ya ke faruwa wanda ainihi ba haka bane.

Agyole Abeh tare da kwamandan rundunar soji dake Kaduna Janar Ismaila Isa sun koma yankin da zama domin ganin an shawo kan matsalar rikicin yankin.

Share.

game da Author