Mu na kira ga Jami’an tsaro da su hana Ali Sheriff amfani da ofishin mu – PDPn Makarfi

0

Sakataren jam’iyyar PDP Dayo Adeyeye wanda dan bangaren PDPn Makarfi ne yace zuwa ofishin jam’iyyar PDP da Ali Modu Sheriff yayi ba dadidai bane.

Yace Kamar yadda ya sani zuwan Ali Modu ofishin jam’iyyar ya saba ma doka kuma ya kamata a tuhumeshi akan hakan.

Yace zuwan Ali ofishin jam’iyyar ba tare da izini ba bai dace ba domin gaba daya ginin ofishin a kulle yake, sannan ofisoshin da suke ciki suma a kulle suke.

“Ina tabbatar muku da cewa mukullen ofishin jam’iyyar duka suna hannun shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar, saboda haka ta yaya ya shiga ofishin idan ba balle kofofin sukayi ba kuma hakan ya na nuni da rashin kamala da ga garesu da kuma karya doka.

Yace bangarensa sun dauka cewa Ali Sheriff zai jira har sai an yanke hukuncin karar da suka shigar kotun koli tukuna kafin ya fara tunanin ko zai koma jam’iyyar ko A’a.

Yayi kira ga Ali Sheriff da ya yi maza maza ya tattara inashi-inashi ya kaurace ma ginin jam’iyyar tun da wuri sannan ya roki jami’an ‘yan sanda da su hana Ali shiga Shelkwatan jam’iyyar da sunana wai zai fara aiki.

Share.

game da Author