Hukumar EFCC ta kwato naira biliyan 3 ajiye a gidan Andrew Yakubu

0

Hukumar EFCC ta kwato wasu kudade da ya kai naira biliyan uku da suke ajiye a gidan tsohon shugaban Kamfanin mai na kasa (NNPC) Andrew Yakubu.

An samo kudaden ne gidansa da ke Kaduna.

Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ne ya sanar da hakan a wata zama da majalisar wakilai ta gaiyace shi da ya zo ya yi mata bayanai akan kasafin kudin hukumar ta 2017.

Ibrahim Magu yace sun samu kudaden ne wuri na gugan wuri har na dala miliyan 9.2 da fan 750,000 ajiye a gidan na sa.
Yace bincike ne ya kai su gidan inda sukayi kicibus da wadannan magudan kudade.

Bayan haka ya sanarwa ‘yan majalisar cewa hukumar EFCC din ta kwato wasu kudade da yakai naira biliyan 1.2 daga hannun wani ma’aikacin gwamnatin tarayya.

Share.

game da Author