Babu wani dan Adam da ya fi karfin jarabawar Allah, mu ci gaba da yi ma Buhari addu’a – Inji Atiku Abubakar

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kira ga ‘Yan Najeriya da su cigaba da yi ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a domin samun lafiya da nasara a mulkin sa.

Atiku yace babu wani dan Adam da ya fi karfin jarabawar Allah, saboda haka mai makon mugayen fata da wasu ke yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Addu’a ne kawai zai fi a gareshi daga gare mu baki daya.

Ofishin tsohon mataimakin shugaban kasar ne dake Abuja suka fitar da wannan sanarwa a madadin Atiku Abubakar
Sanarwan ta kara da cewa Atiku ya yi addu’an Allah ya dawo mana da shugaban kasar Muhammadu Buhari lafiya domin ci gaba da ayyukan da wannan gwamnati ta sa a gaba.

Share.

game da Author