Kungiyoyin Jama’atu (JNI) da na Kiristocin Najeriya (CAN) sun yi kira ga mutanen Najeriya da su taya shugaban kasa Muhammadu Buhari da addu’a domin Allah ya bashi lafiya akan ciwon da yake fama da shi.
Wani jigo a kungiyar CAN Kwamkur Samuel yace kungiyar tayi kira ga majami’un kiristoci da ke kasarnan da su saka shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin addu’o’in su, Allah ya bashi lafiya.
Kungiyar Jama’atu ita ma ta yi irin wannan kira ga musulmai da su saka shugaban kasa a cikin addu’o’insu.
Sakataren kungiyar Dr. Khalid ya yi kira ga limamen masallatan juma’a da su saka shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin hudubobinsu ta gobe sannan a yi masa addu’o’i.
Allah ya kara wa Shugaban kasa lafiya. Amin.
Discussion about this post