Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ci gaba da zama a kasar Ingila har na tsawon wasu ‘yan kwanaki.
Fadar shugaban kasa ne ta sanar da hakan a wata sako da mai ba shugaban kasa shawara akan harkar watsa labarai Femi Adesina ya sanya wa hannu.
Buhari ya rubuta sabuwar wasika zuwa majalisar tarayya domin sanar musu da neman karin kwanaki a hutun na sa.
Likitoci ne suka shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dan kara kwanaki domin samun sakamakon gwaje gwajen da akayi masa a kasar Ingila.
Yau ne dama ake sa ran dawowar shugaban kasa Najeriya.