Gwamnan jihar Barno Kashim Shetima ya amince da rusa shugabannin kwamitocin riko na kananan hukumomin jihar.
Kwamishinan kananan hukumomin jihar Zanna Usman ne ya sanar da hakan a garin Maiduguri.
Zanna ya ce gwamnan ya amince da hakanne bayan shugabannin sun cika adadin zamansu a kujerun shugabancin kananan hukumomin.
Ya Kara da cewa dukkansu sun kammala adadin watanni shida da dokar kananan hukumomin jihar ta bayar.
Gwamnatin ta umarci kowannensu ya mika ragamar mulkin karamar hukumarsa a hannun sakataren karamar hukumar kafin gwamnati ta nada sababbi.