Wani jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan jiragen sama Femi Fani Kayode yace ba za su amince da hukuncin da kotun daukaka kara tayi na halartar wa Ali Modu Sheriff kujeran shugabancin jam’iyyar PDP ba.
Fani Kayode yace Ali Sheriff dan jam’iyyar APC ne kuma yana wa jam’iyyar aiki ne.
Yace Ali Modu yana gyara wa APC hanya ce kawai domin su sake lashe zabukkan Shekara ta 2019.
Yace baza su bi Ali Modu Sherriff ba saboda sun gano ba jam’iyyar bace a zuciyarsa.
Duk da cewa Femi Fani Kayode ya nuna rashin jin dadin sa akan nasarar da Sheriff ya samu a kotun daukaka kara dake jihar Ribas, Sanata Ben Bruce ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su amince da hukuncin kotun sannan su mara ma Ali Modu Sherriff baya domin cigaban jam’iyyar.