Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace iyalansa ba za su gaji wani abun Kirki daga gareshi ba ko bayan bashi da rai.
Buhari ya ce ya shawarci ‘ya’yan sa da su zake su nemi ilimi domin shine kawai zai sa su iya rike kansu.
Buhari ya tabbatar da ganin cewa ‘ya’yan sa mata duk sunyi karatu har zuwa matakana jami’a.
Wani Farsesa ne dan kasar Amurka ya fadi hakan a wata littafi da ya rubuta akan Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai suna “Muhammadu Buhari: “Gwagwarmayar shugabanci a Kasa Najeriya” wato “Muhammadu Buhari: The Challenges of Leadership in Nigeria,” a turance.
Kamar yadda bayanai suka nuna akan kaddarorin da shugaba Buhari ya mallaka kuma ya mika wa hukumar kula da da’ar ma’aikata, Bayanai ya nuna cewa Buhari na da mallakin gidaje biyar ne kacal, Biyu a garin Daura, 1 a Kano, daya a Kaduna sannan da wadansu filaye biyu da bai gina su ba.
Bayan haka kuma yana da mallakin garken shanu, tumakai da awakai.
Haka kuma a bayanan da ya mika, Miliyan 30 ce kawai ya mallaka a asusun ajiyarsa dake bankin Union.
Buhari yana da motoci biyu da ya siya da kudinsa, banda wadanda aka bashi kyauta bayan harin da aka kai masa a Kaduna da kuma wadanda ya ke samu daga gwamnatin tarayya a matsayinsa na tsohon Shugaban kasa.
Discussion about this post