Aisha Buhari ta dawo Najeriya daga aikin Umrah

0

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta dawo daga aikin Umrah yau.

Aisha ta sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja in da uwargidan shugaban majalisar dattijai Toyin Saraki da matan gwamnonin jihar Kebbi da na Kogi suka tarbe ta.

Da take jawabi ga manema labarai a filin jirgin Aisha Buhari ta gode wa ‘yan Najeriya sannan ta gode ma Allah da ya dawo da ita lafiya.

“ Na yi ma Najeriya da shugabanninta addu’a” Aisha ta ce.

Share.

game da Author