Bani da wani dan wasa da na fi so a farfajiyar fina-finan Hausa – Inji Maryam Booth

1

Maryam Booth fitacciyar jarumace a farfajiyar fina-finan Hausa wanda kwarewarta ya sa ta samu lambobin yabo da dama a harkar.

A hiran da tayi da gidan jaridar PREMIUM TIMES, Maryam tayi bayani akan shiri da take dashi na bude makarantar koyar da shirya fina-finai a jihar Kano, da kawancenta da abokanan aikinta da sana’ar da takeyi bayan harkar fina-finai.

Sannan kuma ta yi tsokaci akan jita-jitan da ake ta yadawa wai basa jituwa da Rahama Sadau, kawancen ta da Nafeesat Abdullahi da dai sauransu.

PT: Kina daya daga cikin mata 3 a farfajiyar fina-finan Hausa da suke da mabiya masu yawa a shafin sada zumunta na Instagram, me ne ne sinadarin samun hakan?

MARYAM: Abin da na sani shine ban dauki kaina a komai ba, ni kowa nawa ne, duk inda Allah ya hada ni da mutum zan daukeshi kamar da ma can na san shi ne.

Ina ganin hakanne ya sa mutane da yawa suke kauna ta kuma yasa na ke da yawan mabiya a shafunan sa da zumunta a yanar gizo.

PT: Yaushe kika fara fitowa a fina-finan Hausa?

MARYAM: Na fara fitowa a fim ne tun ina da shekara 8 kuma na girma na ga mahaifiyata na yin fim, kila shi ya sa na fara son aikin. A yanzu haka ina da shekara 23 a duniya.

PT: Ba’a ganin ki a fina-finai a ‘yan kwanakin nan, ko me yasa?

MARYAM: Dalilin daya sa aka rabu da gani na a fina-finai shine saboda na koma makaranta amma akwai wasu fina-finan da za su fito kwanan nan wanda na fito a cikin su.

PT: Kin kusa gama karatun?

MARYAM: Na gama digirina na farko a fannin kasuwanci daga kwalejin Mantissa da ke kasar Malaysia da kuma karamar difloma daga jami’ar Bayero dake Kano.

Yanzu haka ina yin karatun digirita ta biyu wato (Masters).

PT: Kina ganin bai kamata ace kin yi watsi da harkar fina-finai ba kin fara aiki kawai ganin irin wadannan karatu da kika yi haka?

MARYAM: Kamar yadda na fada maka, zai yi wuya in daina yin fim domin abin da nake so kenan. Duk da haka akwai ‘yan sana’o’I da nake yi kamar yanzu haka ina da shagon kwalliya da na bude a Kano mai suna MBooth Beauty Palour da dai saauransu.

Kuma duk da haka ina shirin bude makarantar koyar da sana’ar shirya fina-finai.

PT: Mutane sun ce ba kwa ga maciji tsakanin ki da Rahama Sadau

MARYAM: A’a wannan zancen teburin mai shayi ce. Bari in gaya maka, na yi farinciki sosai lokacin da Ali Nuhu ya gabatar da Rahama Sadau a wurina. Na yi farin ciki sosai domin na sami ‘yar uwa wace shekarun mu ya kusan zuwa daya a farfajiyar fina-finan Hausa a wannan lokacin.

Ban taba samun matsala da ita ba ko kuma ta samu da ni.

PT: Kawar ki ce ta kut da kut ko A’a?

MARYAM: Bani da kawa a farfajiyar finafinan Hausa sai dai abokan arziki. Ko da yake ina muamula sosai da Nafeesat Abdullahi domin jinin mu ya hadu.

PT: Za ta iya zama kawarki na kut da kut Kenan ko?

MARYAM: Eh, ina ganin haka domin jinin mu ya hadu sosai (dariya)

PT: Me za kice akan koran da akayi ma Rahama Sadau ?

MARYAM: A ganina hakan ba bu dadi musamman ganin inda kake sa’ar kace. Sai dai kuma dole wata rana mu girbe abin da muka shuka musamman a farfajiya irin ta mu wanda al’ada da addini suke manne da duk wani abu da za mu gudanar.

Hakan dai zai zamo ma na baya darasi cewa komai zakayi kayi taka tsantsan akai amma babu dadi kam koranta da akayi. Abin da zan iya fada kenan.

PT: Za ki iya auran dan fim?

MARYAM: A’a amma idan hakan ya faru duk daya ne.

PT: Misali idan aka sa miki bindiga aka ce ki zabi wani dan fim, wa za ki zaba?

MARYAM: A gaskiya babu kowa.

PT: Yaya kike ji lokacin da kike fim daya da mahaifiyar ki?

MARYAM: Mun yi fim tare da yawa amma duk da haka na kanji kamar da gaske ne ba fim ba (dariya)idan muna tare.

PT: Menene zumuntar ki da Ramadan Booth, shi kanin ki ne ko wa?

MARYAM: A’a Ramadan dan uwana ne , muna da zumunta.

PT: Me ki ke yi idan ba kya aikin fim?

MARYAM: Kwaliya.

PT: Wani dan wasa ne yafi burge ki?

MARYAM: Ban da kowa yanzu domin wanda ya fi burgeni shine Rabilu Musa Ibro kuma ya rasu. Allah ya jikansa Amin.

Share.

game da Author