El-Rufai yayi tir da rusa dashen sabon bariki da aka yi a Zangon kataf

1

Gwamnan Jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai ya yi tir da rusa dashen ginin da gwamnati tayi domin samar da sabuwar barikin sojoji a yankin Kudancin Kaduna.

Wasu da ba’asan ko su wanene ba sun rusa dashen ginin da gwamna El-Rufai yayi tare da babban hafsan sojojin Najeriya Tukur Burutai domin samar da sabuwar bariki a yankin.

Gwamnan yace duk wadanda suke aikata wannan aiki ba sa kyauta ma jihar musamman yadda gwamnati ta ke kokarin ganin ta kawo karshen rashin zaman lafiyar da yaki ci yaki cinyewa a musamman yankin kudancin Kadunan.

El-Rufai yace gwamnatinsa ba za tayi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wani da aka kama da laifi wajen aikata wannan aiki.

Ya kara da cewa gwamnati ba za ta kyale duk wani da yake yi ma jihar kwantar bauna ba wajen ganin ya ruguza shirye-shiryen gwamnati na samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Share.

game da Author