Mashahurin kamfanin nan da ya yi suna wajen bin-diddigin gano kintacen yawan marasa aikin yi a faɗin duniya, wato KPMG, ya yi kintacen cewa a cikin 2023 yawan marasa aikin yi a Najeriya zai kusa yin kankankan da yawan masu aikin yi da ƙasar ke da su.
KPMG ya ce zuwa ƙarshen 2022, yawan marasa aiki a cikin majiya ƙarfin Najeriya ya kai kashi 37.7. “Amma a kintacen yadda abubuwa ke tafiya saboda wasu dalilai da ke faruwa, yawan marasa aikin yi zai iya kai kashi 40.6 kafin ƙarshen 2023.” Inji KPMG.
A cikin wani rahoto da KPMG ya fitar baya-bayan nan, ya ƙara da cewa hatta tsadar rayuwa da tashin gwauron zabin kayan abinci ba zai sauko ba, zai ci gaba da kasancewa sama da kashi 20 bisa 100, amma ba zai koma ƙasa da kashi 20 bisa 100 ɗin ba.
Idan za a iya tunawa dai Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Najeriya, wadda mallakar gwamnatin tarayya ce, ta ce yawan marasa aikin yi a ƙarshen 2020 ya kai kashi 33.3 na adadin majiya ƙarfin ‘yan Najeriya.
KPMG a na sa ɓangaren ya ce babban abin da ke sa rashin aikin yi zai ci gaba da ƙaruwa a cikin 2023 har zuwa ƙarshen shekarar, shi ne rashin masu zuwa jari mai tsoka a harkokin masana’antu, manyan kamfanoni a ƙasar.
Wani ƙarin dalili kuma shi ne yadda tattalin arzikin ƙasar ke tafiyar hawainiya, wani lokaci kuma ma har tafiyar-kura ya ke yi.
KPMG ya ce lamarin fa akwai tsorataswa a Najeriya, domin kowace shekara aƙalla ana samun matasa miliyan 5 da su ka kai munzilin neman aiki, kuma ko sun nema, ba samu su ke yi ba.
Matsalolin da ke ƙara haifar da munin lamarin har ila yau sun haɗa da tsare-tsaren marasa fa’ida da Gwamantin Tarayya ke bijiro da su, ko kuma masu fa’idar amma gwamnati ta kasa cika alƙawarin aiwatar da su, ko kuma a aikwatar da tsare-tsaren ba ta hanyar da ta dace ba.
Akwai kuma matsalar tsaro, matsalar harkokin sufuri ingantattu, matsalar wadataccen noman kayan abincin da kasuwannin cikin gida da na duniya ke buƙata, yaƙin Ukraniya da Rasha da sauran dalilan da ba a bayyana ba.
Discussion about this post