Jam’iyyar PDP ta dakatar da wasu gaggan ‘yan jam’iyar da ta ke zargi da yi wa jam’iyyar zagon kasa da cin amanar jam’iyyar.
Jam’iyyar ta dakatar tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani wanda sanata ne yanzu daga jam’iyyar bisa zargin cin amana.
Wadanda aka dakatar sun hada da Chris Ogbu daga jihar Imo, Ayeni Funso (kiti Ta Arewa) da Ajijola Lateef Oladimeji (Ekiti Ta Tsakiya).
Sauran sun hada da Emiola Jennifer (Ekiti Ta Kudu), Ajayi Samuel (Ekiti Ta Arewa), Olayinka Olalere (Ekiti Ta Tsakiya), Akerele Oluyinka (Ekiti Ta ArewaI) da Fayose John – (Ekiti).
Sakataren Jam’iyyar na Kasa Debo Ologunagba ya sanar da haka a sanarwar da ya fitar ranar Juma’a.
Ologunagba ya ce dukkan su wadanda aka dakatar sun karya dokar jam’iyyar da hakan ya sa aka dauki mataki akai.
Nnamani bai boye alakar sa da tsohon gwamnan jihar Legas , Bola Tinubu ba.
Ya rika fitowa a baya yana nuna goyon bayan sa ga takarar Tinubu shugabancin Najeriya a APC.
Discussion about this post