Ministan Albarkatun man fetur, Timipre Sylva ya karyata raderadin wai gwamnati ta kara farashinlitan mai.
Karamin ministan albarkatun man fetur Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da babban mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa Horatius Egua ya fitar.
Minista Sylva ya yi magana ne yayin da Najeriya ke ci gaba da yin layin neman mai a gidajen mai sannan a daidai lokacin da rahotanni ke nuna karin farashin man fetur.
Sylva ya yi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai amince da karin farashin man fetur ba.
“Babu wani dalili da zai sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karya alkawarin da ya yi a baya na cewa ba zai amince da karin farashin man fetur a wannan lokaci ba,” inji ministan.
A cewarsa, shugaban ya damu da halin da ‘yan Najeriya ke ciki, kuma ya sha yin bayyana cewa ya fahimci kalubalen da mutane ke fuskanta, kuma ba zai so ya jawo wa jama’a wahala ba.
Wani rahoto da jaridar Guardian ta fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta amince da Naira 185 a matsayin sabon farashin man fetur kan kowace lita.
Jaridar ta ruwaito cewa an sanar da farashin da aka amince da shi ga manyan ‘yan kasuwa a cikin wata sanarwa da safiyar Alhamis.
Amma Minista Sylva a ranar Juma’a ya yi ikirarin cewa gwamnati ba za ta amince da duk wani karin kudin mai ba a asirce ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.