Shugaban NNPCL Mele Kyari ya bayyana cewa ba fa zai yiwu a ci gaba da sayar da litar fetur ɗaya kan naira 170 ba.
Kyari ya yi wannan gargaɗi ne mai nuna alamar shirin fara sayar da litar fetur da tsadar gaske, ko kuma shirin cire tallafin fetur ɗungurugum.
Ya yi wannan furuci a daidai lokacin da ake tsakiyar wahala da ƙarancin fetur a birane, garuruwa da ƙauyukan ƙasar nan.
A Abuja ta kai a cikin unguwanni mabakin manyan titina yara matasa ‘yan bumburutu na sayar da fetur a gefen titina.
Yawancin gidajen mai babu kowa kuma babu komai. Waɗanda ke da fetur kuwa za ka samu dogon layin da wasu direbobin kusan yini su ke yi kafin su samu su saya.
‘Yan bumburutu na sayar da lita 10 kan Naira 3,500. Hakan kenan duk lita ɗaya ta tashi Naira 350.
Shi kuwa Kyari cewa ya yi ba zai yiwu gwamnati ta ci gaba da sayar da fetur a haka ba, “saboda kuɗin ladar dako da saukalen fetur ɗin idan an shigo da shi, ya nunka kusan sau uku.’
Ya yi wannan bayani a Taron Kwamitin Yaƙi da Rashawa na Majalisar Wakilai ta Ƙasa, a Abuja.
Ya ce NNPCL na sayar da lita ɗaya ga kan naira 113, sannan a sayar da lita ɗaya 165 a gidajen mai. “Inda matsalar ta ke, a yanzu saboda tsadar kuɗin saukale tallafin kowace lita ɗaya ya kai naira 290.”
Ya ce saboda wannan gagarimar matsala ta sa tilas ba a iya daƙile sumogal ɗin fetur ana fita da shi waje takan iyakokin Najeriya.
“Shi ya sa a kullum ake fama da masu yin fojare ɗin takardun neman tallafin mai da sauran baddalallun bayanai.
Discussion about this post