Yayin da aka Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta buga gangar fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a ranar 28 Ga Satumba, hankulan jama’a ya karkata ne kacokan kan ‘yan manyan barade huɗu: Akwai ‘gardi’ da kuɗi kuma mai ɗaurin gindin Gwamnantin Buhari, wato Bola Tinubu, wanda shi ne ɗan takarar PDP, akwai ‘duna maso-rai-wawa’, Atiku Abubakar na PDP, wanda an sha bugawa da shi ana kai shi ƙasa, amma har yau bai fasa ba, kuma bai gaza ba.
Akwai kuma ‘gojirgo namijin giginya’, wanda ake wa kallon ba shi da ‘ya’yan da za su taya shi yaƙin kare mutuncin shan kashi a filin daga, wato Peter Obi. Amma kuma ana ganin ya na da sojojin baka. Sai kuma ‘jirgin sama, ko mace tsari ta san rugugin ka’, wato Rabi’u Kwankwaso.
Daga cikin huɗun nan, babu wanda bai yi irin shirin sa ba bakin gwargwado. Haka kuma babu wanda ba shi da matsalar sa daidai gwargwado.
Sai dai a yau, matsalar Atiku Abubakar na PDP ce abin dubawa tukunna, kafin a kai ga sauran.
Atiku ya fara cin karo da matsala tun kwana ɗaya bayan zaɓen fidda-gwani, inda Gwamna Nyesom Wike da wasu gwamnonin Kudu huɗu, sai kuma Samuel Ortom na Benuwai, su biyar su ka ƙi shiga shirgin Atiku, bisa zargin rashin adalci.
Tun daga lokacin kuwa har yau PDP na fama da cutar mashaƙon da dole sai an warkas da ita matsawar ya na so ya yi nasara a cikin ruwan sanyi.
Fara kamfen a Jihar Akwa Ibom ba tare da gwamnoni biyar ba, babbar matsala ce ga Atiku.
Jihohin da gwamnonin su ka ƙaurace wa Atiku sun haɗa har da Oyo, jiha ta uku wajen yawan jama’a, bayan Legas da Kano. Sai kuma Jihar Ribas, waɗanda Oyo da Ribas ɗin duk PDP ce ke da rinjaye. Gaba ɗayan jihohi biyar ɗin da su ka ƙaurace wa zugar yaƙin Atiku za su iya samar masa ƙuri’u miliyan 2.5, ko sama da haka.
Wasu na kallon cewa Atiku ya yi damaga ko kwakyariya wajen ɗaukar Gwamna Ifeanyi Okowa matsayin ɗan takara. Kamata ya yi a ce ya ɗauki Wike.
Akwai masu ganin cewa shi kan sa Atiku bai kamata ya fito takara ba, domin wai akwai yarjejeniyar cewa ɗan Kudu ne zai yi wa PDP takara.
Sannan kuma gungun su Wike a yanzu su na so lallai sai shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu ya sauka an naɗa ɗan Kudu shugabancin jam’iyya.
Cikin wannan makon kuma wasu dattawan PDP sun nemi a sake Babban Kwamandan Yaƙin Atiku Abubakar, a naɗa Raymond Dokpesi. Kuma sun yi zargin cewa a cikin Mataimakan Kwamandoji akwai waɗanda babu kishin jam’iyya har cikin zuciyar su.
Ya kamata Atiku ya sake sabon lale tun kafin a kai ga ranar buga bugun fenaritin sa na ƙarshe, domin daga 2023 dai ba zai sake fitowa ya ce zai yi takara kuma. Sai dai ya haƙura ya yi zaman lissafin asarar da ya yi a takara huɗu da ya yi ba tare da nasara ba.
Tangal-tangal Ɗin Jirgin Yaƙin Atiku Abubakar:
Jirgin yaƙin PDP na tangal-talgal saboda gwamnoni biyar sun ƙi hawa a yi lodin kamfen tare da su.
Duk da cewa jam’iyyar PDP ta ƙaddamar da kamfen ɗin yaƙin neman zaɓen 2023 a Akwa Ibom cikin nasarar tara ɗimbin jama’a, ƙaurace wa gangamin da gwamnoni biyar su ka yi ya nuna har yanzu akwai jan-aiki ga Atiku sosai kafin ya dangana da kujerar shugaban ƙasa.
Gwamnonin guda biyar da ba su halarci taron ba, sun haɗa da Nyesom Wike na Jihar Ribas, Seye Makinde na Jihar Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Ikpeazu Okozie na Abiya sai kuma Samuel Ortom na Jihar Benuwai.
Su huɗun su na goyon bayan Wike ne, wanda ya jagorance su bijire wa PDP bayan an tsayar da Atiku takarar shugaban ƙasa.
Su biyar ɗin dai su na neman tilas sai shugaban PDP, Iyorchia Ayu ya sauka a naɗa ɗan Kudu, domin a tabbatar da adalci a shugabancin PDP.
Gangamin wanda PDP ta yi a Filin Wasa na Godswill Akpabio International Stadium, ya cika fal da magoya bayan PDP, inda a wurin Atiku ya sha alwashin cewa idan aka zaɓe shi, to za a yi bankwana da talauci da matsalar tsaro da rashin aikin yi a Najeriya.
Idan ba a manta ba, waɗannan gwamnoni biyar ba su halarci taron ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na PDP ba.
Masu bibiyar lamarin siyasa na ganin cewa PDP za ta iya fuskantar matsala matsawar ba ta sasanta da gwamnonin biyar ba.
Su Wike dai su na jin haushin yadda ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma Shugaban PDP Iyorchia Ayu duk su ka fito daga yankin Arewa.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da rundunar yaƙin Bola Tinubu na APC ta ce, rikicin da hasalallun gwamnonin PDP ke yi da shugabannin jam’iyyar su, alheri ne ga APC.
Rundunar Yaƙin Tinubu 2023 ta ce turnuƙun rikicin da wasu hasalallun gwamnonin PDP ke yi da shugabannin jam’iyyar su, alheri ne ga jam’iyyar APC.
CIkin wata sanarwa da ɗaya daga cikin Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Tinubu, Festus Keyamo ya fitar a ranar Asabar, ya ce rikicin da ke faruwa a cikin PDP ya nuna cewa jam’iyyar ba za ta iya riƙe mulkin Najeriya ba, tunda har yau ta kasa ma sasanta rikicin da ke cikin gidan ta.
Keyamo ya ce PDP ba za ta iya haɗa kan Najeriya ba, tunda ta kasa haɗa kan iyayen jam’iyyar PDP ɗin.
Hasalallun gwamnonin dai bisa jagorancin Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, har yau sun ƙi goyon bayan takarar shugabancin ƙasa da Atiku Abubakar ke yi, bisa dalilin cewa babu adalci wajen raba muƙaman jam”iyyar, saboda an damƙa shugabancin PDP ga ‘yan Arewa, inda kuma a yankin ne ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya fito.
Gwamnonin dai sun gindaya cewa kafin su fara goyon bayan Atiku, tilas sai Shugaban PDP, Iyorchia Ayu ya sauka an naɗa ɗan Kudu, domin a yi adalci.
Sannan kuma zargin da Wike ya yi wa Ayu kwanan nan, cewa ya raba wa shugabannin jam’iyyar cin hanci, kuma ya karɓi naira biliyan 1 a hannun wani a Legas, ya ƙara jefa PDP cikin ruɗani.
Keyamo ya ce har yau jam”iyyar PDP ba ta tuba daga ɗabi’ar ta na wawurar kuɗaɗe ba. Don haka ba za ta yaudari ‘yan Najeriya ba a zaɓen 2023.
“Ai mu rikicin da wasu gwamnonin PDP ke yi da shugabannin jam’iyyar su, alheri ne a gare mu. Sun kasa haɗa kan su, kuma rikicin wuru-wurun kuɗaɗe ya ƙara dagula PDP. Hakan ya nuna har yau ba su tuba daga ɗabi’ar su ta sata ba.
Keyamo ya ƙara caccakar PDP cewa sun bi son ran Atiku, sun ƙi bai wa Kudu takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, kamar yadda su ka yi yarjejeniya a baya.
Discussion about this post