Ɗan takarar Sanata na shiyyar Kaduna Ta Tsakiya karkashin APC, Mohammed Abdullahi, da aka fi sani da Dattijo, ya bayyana jin daɗin sa ga daukar mataimakiyar gwamnan Kaduna, Hadiza Balarabe mataimakiyar sa a zaben 2023.
” Ni ɗannan na fi kowa farin ciki da murnar ɗaukar Hadiza Balarabe mataimakiyar gwamna da ɗan takarar gwamna Uba Sani yayi. Yin hakan nuni ne cewa ana tafiya tare kuma tare za akai ga ci da nasara. Hadiza tana da kwarewa da sanin yadda ayyuka suke tafiya a jihar Kaduna wanda hakan zai sa a samu tafiya da ɗorewa mikakkiya idan gwamnati sabuwa ta dare karagar mulki.
Bayan haka Dattijo ya yabawa wa ƴan jam’iyyar da shugabannin ta da suka yi zurfin tunani wajen zaɓin ta ta yi wa Uba Sani mataimakiyar gwamna.
Akarshe yayi kira ga ƴaƴan jam’iyyar da su yi aiki tuƙuru domin samun nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.
Discussion about this post