Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 490 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -142, FCT-60, Bayelsa-54, Rivers-39, Delta-37, Oyo-30, Kaduna-26, Imo-23, Enugu-19, Kwara-17, Gombe-11, Ondo-10, Bauchi-8, Ogun-7, Borno-6, Benue-1.
Yanzu mutum 17,148 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 5,623 sun warke, 455 sun rasu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 7,103, sai FCT – 1, 247, Kano – 1, 137, Ogun – 559, Edo – 580, Oyo – 507, Rivers – 489, Kaduna – 446, Borno – 438, Katsina – 414, Bauchi – 410, Gombe – 410, Jigawa – 317, Delta – 267, Ebonyi – 162, Abia – 166, Kwara – 150, Plateau – 156, Nasarawa – 172, Imo – 136, Sokoto – 132, Zamfara – 76, Anambra – 65, Ondo – 64, Yobe – 55,Kebbi – 57, Enugu – 57, Osun – 50, Niger – 56, Akwa Ibom – 48 Adamawa – 42,, Benue – 34, Bayelsa – 32, Ekiti – 30, Taraba – 18, da Kogi – 3.
Discussion about this post