Amfanin gwamnati shine ta samar da tsaro a cikin al’umma. Shine abinda ya bambanta alqaryar da take da gwamnati da alqaryar da ta rayu babu gwamnati lokacin da duniya take ‘yar qauye (Primitive society). Haka Thomas Hobbes yace.
Babu abinda ya kai rayuwa dadi. Don ko Bahaushe ma cewa yayi, “Rigimar duniya da mai rai ake yi”. Shiyasa duk gwamnatin da ta kasa samar da tsaro, ta samu matsala. Tsaro abu ne wanda yake samar da komai a cikin alqarya. Duk sanda akace babu shi, to akwai matsala dari bisa dari saboda babu abinda zai tafi daidai.
Idan babu kwanciyar hankali, kasuwanci baya tafiya, kimiya da fasaha basa gudanuwa sosai, addini a tsorace za a dinga yi, kwadago baya yiwuwa. Shiyasa talauci yake qaruwa a yankunan da tsaro yayi qaranci. Kwanciyar hankali ce take samar da wanzuwar arziki.
Idan tsaro ya lalace an shiga uku, saboda babu zancen cigaba. Kula da rayuwar mutane ta zama a hannunsu. Kuma hakan gazawa ce ga gwamnati wacce itace take da jami’en tsaro da duk wasu abubuwan kare rayuka da dukiyoyin mutane.
Halin da Arewacin Najeriya take ciki yana bayyana gazawar gwamnati. Rayuwar mutane ta zama kamar ta sauro. Irin wadannan abubuwan idan suna faruwa a wani waje, idan ba a dauki mataki ba zai iya zuwa inda ba a zato. Idan har abun ya gagari gwamnati, to gaskiya an kusa komawa “anarchy”. Anarchy shine lokacin da babu gwamnati.
Arewacin Najeriya ta shiga rudani, idan ba an tashi da gaske ba wajen tabbatar da adalci, to lallai muna cikin rikici. Don adalci ne kawai zai kawo saukin abubuwa. Mataki na farko, sai an samarwa da matasa aikin yi sannan za a samu sauki.
Talauci yana da tasiri wajen haifar da rashin tsaro. Amma saidai nayi mamaki da naji mai girma sarkin musulmi yana cewa ba talauci bane yake haifar da rashin tsaron Arewacin Najeriya. Allah ya kara masa lafiya, talaucin shima yana da gudunmuwa. Duk sanda matasa suka zama basu da aikin yi, gaskiya akwai matsala goma-goma.
Annoba ce barin matasa basu da aikin yi, saboda wasu daga cikinsu masu rauni zasu baiwa kansu aikin yi ta kowacce hanya. Idan har shugaba Buhari zai cigaba da tunani akan matasa. Idan za a cigaba da samar musu da ayyukan yi, za a samu saukin irin wadannan tashin hankalin idan Allah yaso.
Allah ya bamu zaman lafiya.
Discussion about this post