Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’an ta sun kama wasu mutane 7 da take zargi ‘yan kungiyar asiri ne a jihar.
Jami’in hulda da jama’a ta rundunar Mansir Hassan ya sanar da haka ranar Talata.
Ya ce dakarun sun kama wadannan mutane ranar 6 ga Afrilu bayan wasu mutane sun sanar da jami’an tsaron aiyukkan da mutanen ke yi.
“Bayan mun gudanar da bincike, dakarun sun kama wadannan mutane yayin da suke yin tsafi su a tsaunikan Dumbi dake hanyar Zaria zuwa Kaduna.
“Jami’an tsaron sun kama mutum bakwai yayin da sauran suka gudu sannan sun kama makamai da suka hada kananan bindigogi biyu, jarka da wani abu a ciki da suke zargin jini ne da mota kirar Lexus daya.
Kwamishan ‘yan sandan jihar Ali Audu ya hori jami’an tsaron wajen ci gaba da samar da tsaro a jihar domin kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar.
Audu ya yi kira ga mutane da su ci gaba da mara wa jami’an tsaron baya ta hanyar bada bayanan da za su taimaka wajen kama mahara a jihar.
Discussion about this post