A cikin wannan makon Jihar Kaduna ta ɗau zafi a siyasance da ya yi sanadiyyar dakatar da shugaban mata na jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna Maryam Suleiman da aka fi sani da Maryam Mairusau saboda tsananin kauna da biyayya da take yi wa tsohon gwamna, Nasir El-Rufai.
Yanzu dai da alamar komai ya kwaɓe tsakanin gwaskayen biyu tun bayan fallasa irin basukan da gwamnatin da El-Rufai ta ciwo ta bar wa gwamnatin Uba ta ci gaba da biya.
Wannan kalamai da gwamna Uba Sani ya yi ya jawo cecekuce tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Wasu da ya wa na ganin a matsayin Uba Sani wanda ya sha cewa ba shi da ubangida da ya wuce El-Rufai a baya, kuma da waɗanda suke ciki da wajen jihar Kaduna sun san irin kokarin da El-Rufai ya yi ba dare ba rana domin tabbatar da Allah ya ba Uba Sani nasara a zaben 2023 bai da ce ya fito fili ya rika goga wa tsohon gwamnan kashi a fuska ba.
Kowa dai ya san irin yadda El-Rufai ya rika tsinewa Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi saboda sun ki saka hannu ya karɓi bashi daga waje. Daga baya dai da karfin tsiya da kuma karfin gwamnati aka musanya Shehu Sani da Uba Sani don a ciwo wannan bashi da yanzu ya ke kuka a kai.
Abinda Sanata Uba Sani ya fara yi bayan ya zama sanata shine ya tabbatar da an karɓo wannan bashi.
A ganina duk da ba laifi bane gwamna ya fito ya faɗi wa ƴan jihar sa halin da baitil malin jihar ke ciki, a wannan lokaci da shi gwamnan ya ke cewa ya san halin jihar kuma a haka ya tabbatar zai iya mulki ba tare da an samu matsala ba, me ya sa kuma ya karaya bayan ya san komai?
Idan da ya koma ya zauna da mai gidansa El-Rufai ya shawarce sa kila da ya san mafita da dabarun da ake yi idan gwamnati ta samu kanta a cikin wannan hali maimakon fallasa haka da ya yi, tun a jawabin karshe na El-Rufai ya faɗi kuɗin da ake bin jihar, ba sabon abu bane.
Wasu dake nazarin siyasar Kaduna na ganin kamar gwamna Sani ya rasa yadda zai yi mulkin ne, kamar yadda suke cewa a kullum, sai dai ya kamo can, ya saki nan, ya ce haka ya saki can sannan kuma suna ganin akwai wasu a bayan fage dake zuga gwamnan.
Koma dai menene, abinda zai fi dacewa shine gwamna Uba Sani ya tuna baya, ya kuma tuna irin namijin kokarin da El-Rufai ya yi masa, inda ya hakura da kusan a ce ɗan sa wato Mohammed Sani Dattijo, ya mara masa baya, da kuma irin kuri da ya rika yi lokacin kamfen cewa ya san komai kuma zai iya daga inda El-Rufai ya tsaya.
Ko da yake ba a sarki biyu a gari, amma kuma yana da kyau a rika sara a na duban bakin gatari, kuma dai ana wanke tukunya ne don gobe.A siyasa ana haka, irin haka ba farau ba, gwamnoni na faɗa da ubayen gidan su, suma waɗannan kila a shirya nan gaba ko kuma an yi baran-baran kenan.
Discussion about this post