Makiyaya a Karamar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato, sun koka cewa ɓarayin shanu sun arce musu shanu sama da 390 da kudin su ya kai akalla Naira miliyan 300.
Makiyayan sun ce an yi awon gaba da shanun a lokacin da suke kiwo a Bot, Faranti, Anguwan Abuja, Makada da Wumat.
Aminiya ta buga cewa shugaban kungiyar ci gaban Fulani na ‘Gan Allah’ dake karamar hukumar Bokkos Saleh Adamu ya ce sun kai ƙarar abinda aka yi musu zuwa ga kwamandan sashin ‘Operation Safe Haven’ da ke yankin.
“A ranar 4 ga Maris, an yi awon gaba da shanu 71 a yankin Bot, sai a ranar 11 ga Maris, wasu ‘yan bindiga suka saci shanu 93.
“An sace shanu 73 ranar 17 ga Maris sannan aka kara arcewa da wasu a Anguwan Abuja ranar 22 ga Maris.
“An saci shanu 55 a ranar 31 ga Maris da wasu shanu 100 a unguwar Wumat.
A jawabin sa, shugaban kungiyar GAFDAN na Jihar Filato, Garba Abdullahi, ya ce an kai wa ‘yan kungiyar su hari.
“Ana sace mana shanu yadda aka ga dama, baya ga shanu 390 da aka sace a Bokkos, mun kuma yi asarar shanu sama da 100.”
Shugaban ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta kawo ɗauki ga Fulanin jihar Filato.
Discussion about this post