Tun bayan bayyana rasuwar fitacciyar ƴar wasan Hausa, Saratu Gidado da aka fi sani da Daso, ƴan uwa, masoya da abokan aikin ta suka rika yin tururuwa a shafufansu na yanar gizo domin mika ta’aziyyar su.
Daso ta rasu ranar Talata, a gidanta dake Kano.
Fitacciyar ƴar wasar ta yi suna matuka a harkar finafinan Hausa, inda tana daga cikin jaruman da aka fara gwagwarmaya a farfajiyar sama da shekaru 20.
Shugaban Hukumar tace finafinai na jihar Kano, Abba Almustapha tare da abokan aikin ta sun mika ta’aziyyar su ga iyalai da ƴan uwan jaruman.
Za ayi mata sutura da yammacin Talata a Kano.
Discussion about this post