A daidai lokacin da wasu gwamnonin Arewa 10, ciki har da Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ke shirin rankayawa Amurka domin halartar wani taron yadda za a inganta tsaro a Arewacin Najeriya, wasu ‘yan bindiga afka yankin Malumfashi, inda suka sace mata da ƙananan yara a Jihar Katsina.
Gidan Radiyon BBC a Sashen Hausa, ya ruwaito cewa, ”wasu ‘yan bindiga sun kai samame a garin Na-Alma a yankin Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina , inda suka ƙona gidaje, suka kuma sace gomman mutane, galibi mata, har da masu juna biyu, da ƙananan yara.
Rahoton ya ƙara da cewa maharan sun sun kuma yi gaba da wani mutum da a can baya da ‘yan bindigar suka taɓa sare wa hannu da ƙafa, bayan kashe wani mai unguwa.
Bayanai sun ce, hare-haren ‘yan bindigan na baya-bayan nan sun jefa mutane da dama cikin tasku.
“Wani mutumin yankin, wanda ya tsallake rijiya da baya, ya ce suna cikin ruɗani, kuma kashi takwas cikin goma na mutanen garin sun yi ƙaura.
Mutumin ya kuma ce sun shaida wa jami’an tsaro cewa sun samu bayanan sirri na harin da ‘yan bindigar za su kai garin nasu : ” Tun wajen takwas da rabi na dare muka shaida wa jami’an tsaro amman ba su zo ba har sai da mutanen nan suka shiga suka fara harbi, sai dai kawai su ce ga su nan zuwa”, amman ba su zo ba har sai da ‘yan bindiga suka gama ƙone-ƙone da duk abin da za su yi sannan suka zo.”
Mutumin ya ƙara da cewa an yi masu gagarumin ta’adi a harin da ‘yan bindigan suka kai “asarar kam Allah kaɗai Ya san yawanta saboda haka suka bi gida-gida suka ƙona kuma duk manyan gidaje ne suka ƙona sun kuma kashe mai-unguwa.”
Mutumin da muka sakaya sunan sa ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun tafi da wani Alhaji da suka datse wa ƙafa da hannu kwanakin baya, sannan mata sun kai tara waɗanda kowace na da goyo da kuma wasu masu ciki biyu, ” Idan aka haɗa da matan da yaran da wannan alhajin za su kai mutum 20.”
Mutanen yankin sun ce suna fuskantar hare-haren
‘yan bindiga fiye da kowane lokaci.
Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu ya danganta wannan hari da aka kai garin Na-Alma, da cewa hari ne irin na ramuwar-gayya.
Ya ce harin sakamakon halaka wani mutum da ake zargin ƙasurgumin ɗan bindiga ne da muƙarraban sai, waɗanda suka addabi yankin Ƙaramar Hukumar Malumfashi da kewayen ta.
Kuma ana nan ana ci gaba da ƙoƙarin murƙushe wannan matsala ta tsaro a dukkan wuraren da ake fama da ita a Jihar ta Katsina, in ji shi.
Discussion about this post