Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yaba wa sufeto janar ɗin ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun bisa cika alkawari da yayi na aiko ƙarin ƴan sanda zuwa jihar Kaduna.
A sanarwar haka wanda gwamnan da kan sa ya saka wa hannu, kuma ya wallafa a sahfinsa ta Facebook ranar Lahadi, gwamna Sani ya gode wa Egbetokun sannan ya kara da cewa jihar za ta yi amfani da wannan hubbasa na shugaban ƴan sanda domin ƙara kaimi wajen kawo karshen ta’addanci da ayyukan ɓata gari a jihar
” Kyan Alƙawari, cikawa, dama a ganawar mu a baya, Egbetokun ya yi alkawarin turo ƙarin jami’an tsaro zuwa jihar Kaduna da kuma karin kayan aiki.
” Yanzu dai ya cika alkawarin da ya ɗauka kuma jihar Kaduna za ta ci gaba da mara wa ƴan sanda baya domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da take fama da shi a jihar.
Discussion about this post