Shugaban kasa Bola Tinubu ya kammala ziyararsa zuwa ƙasashen waje karo na 12 tun bayan da ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar watanni tara da suka gabata, kuma ya yi kwana 75 a ƙasashen waje.
Tinubu ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima; Shugaban Ma’aikatan sa, Femi Gbajabiamila; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume; Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike; Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje; da Darakta Janar na Hukumar Tsaro, Yusuf Bichi, da dai sauran su.
A ranar farko ta ziyarar tasa, shugaban na Najeriya ya ziyarci gidan adana kayan tarihi na Ƙatar inda ya jaddada muhimmancin rubuta sahihin bayanan tarihin ƙasa, da al’adu, da cigaba, da ƙalubale.
Da yake rangaɗin jibgegen ginin wanda ya kai murabba’in mita 39,994 da ke kewaye da asalin fadar Sheikh Abdullah bin Jassim Al-Thani, shugaban ya ce, “Yana da kyau a rubuta al’adu tun farkon tarihi, al’adun wayewa, haɗin gwiwa, ƙalubale da jajircewar shugabanci.”
Washegari, Tinubu tare da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani sun shaida rattaba hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyi guda bakwai a tsakanin ƙasashen biyu, bayan ganawar sirri da suka yi a fadar shugaban ƙasa dake Doha.
Sun haɗa da: yarjejeniyar haɗin gwiwa a fagen ilimi; sanya ƙa’idojin ɗaukar ma’aikata tare da gwamnatin Qatar; kafa majalisar hada-hadar kasuwanci tsakanin Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa da Masana’antu ta Ƙatar da Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa da Masana’antu da Ma’adinai da Noma ta Najeriya; baya ga yarjejeniyar haɗin gwiwa a fagen matasa da wasanni.
Sauran yarjejeniyoyin sun haɗa da haɗin gwiwa a fannin yawon buɗe ido da harkokin kasuwanci, da kuma yarjejeniyar fahimtar juna da ke yaƙi da haramtacciyar fataucin miyagun ƙwayoyi.
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, da jami’an gwamnatin Ƙatar, Buthaina bint Ali Al Jabr Al Nuaimi, Ministar Ilimi da Ilimi Mai Zurfi; Dr. Ahmad Hassen Al-Hammadi, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje; Sheikh Khalifa Bin Jassim Al Thani, Shugaban Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Ƙatar da Abdullah bin Khalaf bin Hattab Al Kaabi, Mataimakin Sakatare na Ma’aikatar Cikin Gida ne suka sanya hannu kan takardun.
A ranar Lahadi ne Tinubu ya jagoranci Taron Kasuwanci da Saka Hannun Jari na Najeriya da Ƙatar inda ya buƙaci shugabannin masana’antu na Ƙatar da su kai rahoton duk wani jami’in Najeriya da ya nemi cin hanci kafin a bar su su yi kasuwanci a ƙasar.
Ya nanata cewa Najeriya ba zai ƙi cigaba ba saboda abubuwan da suka faru a baya da ke cike da jinkiri na gwamnati da cin hanci da rashawa da ke daƙile sauƙin kasuwanci.
“Kada ku ba da cin hanci ga kowa daga cikin jama’armu. Za ku sami damar zuwa gare ni, ” inji Tinubu.
Shugaban ya kuma tabbatar wa da ‘yan kasuwar duniya cewa Nijeriya a shirye take ta gudanar da harkokin kasuwanci da gaske domin gwamnatin sa za ta yi maganin duk wata maslaha a ƙasar da ke kawo cikas ga masu zuba jari a tattalin arziƙin Najeriya.
Ya kuma yi alƙawarin kawar da duk wasu matsaloli da ke kawo cikas ga harkokin kasuwanci yana mai cewa, “Kada ku bari hasashe ya zama cikas ga shirin ku na saka hannun jari. Najeriya da gaske take game da kawo sauyi a fannin zuba jari.”
Qatar dai ita ce ƙasa ta uku a yankin Gulf da Tinubu ya kai ziyara tun bayan da ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar da kuma ziyarar sa ta 16 a ƙasashen waje.
Ya zuwa yanzu, ya ziyarci birnin Paris na ƙasar Faransa (sau uku); Landan, Birtaniya; Bissau, Guinea-Bissau (sau biyu); Nairobi, Kenya; Porto Norvo, Jamhuriyar Benin; New Delhi, Indiya; Abu Dhabi da Dubai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa; New York, Amurka, Riyadh, Saudi Arabia, Berlin, Jamus da Addis Ababa, Habasha.
Discussion about this post