Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa aƙalla a cikin shekara ɗaya da ta gabata, an karkatar da Dala biliyan 26 daga Najeriya, ta hanyar amfani da asusun manhajar ‘crypto’ ta Binance, ba bisa ƙa’ida ba.
Da ya ke tattaunawa da manema labarai, Gwamnan na CBN ya ce wasu mutane ne a cikin Najeriya da kuma masu amfani da Binance suka karkatar da kuɗaɗen, kuma har yau ba a iya gano ko su wane ne ba.
Tuni dai wannan dambarwa ta yi munin da har Gwamnatin Najeriya ta yanka wa kamfanin ‘crypto’ na Binance tarar Dala biliyan 10.
Gwamnatin Najeriya ta nemi kamfanin ‘crypto’ na Binance ya biya kuɗin tara har Dala biliyan 10.
Wannan hukunci na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da binciken zargin da ake wa Binance da sauran kamfanonin ‘yan ‘crypto’ da hannu wajen haifar da masifar tsadar dala a Najeriya.
Mashawarcin Musamman kan Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka, a wata tattaunawa da ya yi da gidan rediyon BBC, a ranar Juma’a ɗin yau.
Ya ce kamfanin Binance ya ci ƙazamar riba daga “hada-hadar biliyoyin dalolin” da ya yi ta haramtacciyar hanya a Najeriya. Yayin da ita kuma Najeriya ta yi mummunar asara, inji Onanuga.
A wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV ya yi da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, ya ce, “a cikin shekara ɗaya kaɗai, an yi safarar Dala biliyan 26 a manhajar Binance a nan Najeriya, daga wasu mutanen da har yau ba a tantance ko su wane ne ba.”
Dama kuma Mashawarcin Musamman kan Tsaro ga Shugaba Bola Tinubu, Ribadu ya tabbatar da binciken da ake wa kamfanin ‘crypto’ na Binance.
Haka kuma Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya tabbatar cewa kamfanin manhajar ‘crypto’ na Binance na fuskantar bincike daga mahukuntan Najeriya.
A cikin wani bayanin da ofishin ya fitar dangane da tsare shugabannin Binance da mahukuntan Najeriya suka yi, da kuma kulle manyajojin ‘yan ‘crypto’, ONSA ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa ya na jagorantar sauran hukumomin bincike wajen binciken ayyukan Binance.
“Ina tabbatar maku cewa ofishin Mashawarcin Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro na binciken Binance, dangane da matsalar da ta dabaibaye hada-hadar canjin kuɗaɗe. Haka binciken na tafiya tare da CBN da sauran ɓangarorin tsaro,” haka Zakari Mijinyawa, Shugaban Sashen Yaɗa Labaran ONSA ya bayyana wa PREMIUM TIMES, bayan an yi ta neman ƙarin haske a wajen su, a ranar Alhamis.
Sai dai kuma Mijinyawa bai bayar da wani ƙarin haske daga nan ba.
A wani rahoton musamman, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda gwamnatin Najeriya ta cafke shugabannin kamfanin ‘yan ‘Crypto’ na Binance, ta tsare bayan shigowar su Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta tsare shugabannin kamfanin hada-hadar kuɗi ta hanyar intanet, wato ‘Crypto’, wanda aka sani da Binance.
Shugabannin biyu sun diro Najeriya ne bayan a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na dawo da darajar Naira, bayan faɗuwa ƙasa da ta yi warwas a gaban Dalar Amurka da sauran manyan kuɗaɗen waje.
Wata majiya ta shaida da PREMIUM TIMES cewa shugabannin Binance biyu ɗin da aka tsare ɗin, an damƙe su ne bayan shigowar su Abuja da kwana ɗaya, da nufin tattauna mafita su da mahukuntan gwamnatin Najeriya, dangane da garƙame manhajar ‘crypto’ da gwamnatin tarayya ta yi.
Cikin makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa gwamnatin Najeriya ta garƙame manhajar ‘crypto’ na Binance yayin da ruɗanin tsadar Dala ya buwayi ƙasar nan.
Gwamnatin Najeriya ta kulle ‘crypto’ da sauran ire-iren kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe irin sa.
An zarge su da da yi wa Dala kane-kane da maƙarƙashiyar karya darajar Naira da ɗaga darajar Dala.
Majiyoyi da dama daga cikin kamfanonin sadarwa na cikin Najeriya, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa cikin makon jiya Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), ta umarci kamfanonin tarho tarho su kulle manhajojin Binance da sauran su, kuma suka bi umarnin nan da nan.
Baya ga kamfanin Binance, sauran waɗanda aka kulle wa manhajojin rumbun su, akwai Forextime, OctaFX, Crypto, FXTM, Coinbase, Kraken da wasu da dama.
Wata majiya daga ɓangaren Fadar Shugaban Ƙasa ta ce gwamnati ta yanke shawarar garƙame Binance da sauran manhajojin hada-hadar kuɗaɗe na crypto, bayan da wani rahoto ya bayyana cewa masu harƙallar karya darajar Naira da masu karkatar da haramtattun kuɗaɗe na amfani da su wajen aikata manyan laifuka.
Mahukunta sun yi amanna cewa ayyukan daƙa-daƙa da ake aikatawa ta hanyar Binance da su ‘crypto’, ya na ƙara dakushe darajar Naira.
Cikin Satumba, 2023 Hukumar SEC ta barranta kan ta daga mu’amala da Binance Nigeria Limited, tare da cewa shafin hada-hadar ba shi da rajista da hukumar NCC a Najeriya.
Duk da wannan gargadi dai kamfanin na Binance ya ci gaba da harkokin sa, tare da ƙara samun kwastomomi da dimbin mambobi daga Najeriya, musamman yara matasa da kuma masu hada-hadar canjin kuɗi da ɓarayin gwamnati masu karkatar da manyan kuɗaɗe.
Baya ga zargin su Binance na haddasa tsadar Dala, mahukunta na kuma zargin cewa ana amfani da tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta Binance a tsakanin masu aikata muggan laifuka, ciki har da biyan kuɗaɗen fansar waɗanda ‘yan ta’adda su ka yi garkuwa da.
A bayanin da Binance suka yi cikin makon da ya gabata, kamfanin ya ce za su kulle asusun duk wani mai “yin ‘yar burum-burum a manhajar Binance.”
Tsare Shugabannin Binance A Nigeriya:
Majiya ta ce shugabannin biyu sun shigo Najeriya ranar Lahadi, domin su tattauna masalahar a daidai lokacin da aka fara kukkulle su.
A ranar Litinin da rana, shugabannin
Binance sun gana da wasu jami’an tsaro da masu bincike daga Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa a Fannin Tsaro.
Sai dai kuma ganawar ta ba ta haifi ɗa mai ido ba, saboda shugabannin Binance sun ƙi amincewa su bi waɗansu daga cikin umarnin da Gwamnatin Najeriya ta ba su.
Sannan kuma Gwamnatin Najeriya ta zarge su da aikata kasuwanci na biliyoyin Nairori, ba tare da bin ƙa’idar yin rajista ba.
Majiya ta ce gwamnatin tarayya ta nemi Binance su bayar da bayanan hada-hadar kuɗaɗen Naira a manhajar su, har na tsawon shekaru bakwai baya.
Sai dai kuma shugabannin na Binance sun jajirce cewa sai an fara kai su ofisoshin jakadun ƙasashen su da ke Abuja, kafin su bi umarnin gwamnati.
PREMIUM TIMES ta ji cewa Shugabannin na Binance biyu dai ɗaya Ba’Amurke ne, ɗaya kuma Pakistani.
Gwamnantin Najeriya ta samu warantin sammacin kama su da tsare a kotu, har tsawon kwanaki 12.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa EFCC ta karɓi ragamar binciken, su kuma shugabannin na Binance su na tsare a wani gidan saukar baƙi da ke kusa da Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman a Fannin Tsaro.
Discussion about this post