Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen ganin ko ta halin kaka ta kamo da hukunta ‘yan ta’addan da suka kashe sojoji 17 a Delta.
Da ya je jawabi a wurin jana’izar sojojin Tinub ya kara da cewa gwamnati za ta dauki nauyin ya’yan sojojin kaf din su tun daga Firamare har Jami’a.
“Kisan Sojojin Najeriya 17 babban laifi ne kuma babbar asara ce ga ƙasar nan. Waɗanda aka kashe ɗin da sun je ne domin wanzar da zaman lafiya a tsakanin yankuna biyu masu rikici da juna.
“Sojojin da aka yi wa kisan-gillar nan ba su je garin cikin tankunan yaƙi ko ɗauke da manyan bindigogin mashinga ba. Sun je kwantar da hankali ne domin dawo da zaman lafiya a cikin ɓangarorin al’ummomin biyu.
“A madadi na da ƙasar nan baki ɗaya, muna karrama wannan sadaukar da rayuka da su Kwamanda Laftanar Kanar Ali da sauran sojojin 16 suka yi.
“Har abada za a riƙa tuna su a matsayin gwarzayen da suka sadaukar da rayuwar su domin samar da zaman lafiyar wasu. Dukkan su daga yau sunayen su sun shiga cikin gwarzayen sojojin da suka sadaukar da rayukan su wajen kare ƙasar su da kare ‘yan Najeriya, ba tare da damuwa da irin hatsarin da suke fuskanta wajen gudanar da aikin ba.
“Ina sanar da bai wa manyan su huɗu Lambar Girma ta MON. Sauran 13 kuma an ba su lambar OFR.
“Ina miƙa ta’aziyya ga iyalan su da kuma ga ɗaukacin Sojojin Najeriya baki ɗaya. Ina taya ku jimami da alhinin wannan babban rashin da muka yi. Kuma ina addu’a Allah sanyaya zuciyoyin ku. Ya ƙara maku juriyar haƙurin wannan babban rashin da muka yi.
“Babban bashin da waɗannan haziƙan sojoji ke bin mu, shi ne mu tabbatar mun kamo waɗanda suka yi masu wannan mummunan kisa an hukunta su. Kuma za a kamo su ɗin kuma sai an hukunta su. Akwai nauyi kan dattawa da shugabannin yankin Okuama na taya sojoji gano masu hannu wajen yi wa sojojin mu wannan mummunan kisa.
Ina kuma jan hankali sojoji su guji yin ramuwar-gayya kan mutanen Okuama ko maƙautan su, domin tabbatar da ba a hukunta wanda bai ji bai gani ba.
“Wani nauyin da ke kan mu yanzu shi ne kare iyalan waɗannan gwarzayen sojoji da aka kashe.
“Gwamnatin Tarayya za ta bai wa iyalan kowane sojan da aka kashe gida a ko’ina su ke so cikin ƙasar nan. Sannan kuma Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki nauyin karatun ‘ya’yan su har zuwa kammala jami’a.
“Hukumar Sojojin Najeriya ta tabbatar ta biya iyalan su dukkan haƙƙoƙin kuɗaɗen da suka wajaba a biya su, daga nan zuwa cikin kwanaki 90.”
Discussion about this post