Fitaccen mawaki Portable ya ragargaji ɗan daudun nan da aka fi sani da Bobirisky bayan a lashe kyautar mace da ta fi kwalliya a taron karrama ƴan wasan kwaikwayo.
Tun bayan bayyana cewa Bobirisky ne ya lashe kyautar mace da ta fi kyau a wurin taron, mawaƙi Portable ya rika caccakar waɗanda suka shirya bikin.
Portable ya ce ” in banda lalacewa da fitsara, da rashin tarbiyya, ace wai a gasar da mace za ta ci sai wai a baiwa Ɗan daudu kyautar, wai shine ya yi nasara.
” Mutum namiji ya ce ya yi nono, kawai ya zama mace da ƙarfin tsiya, sai kuma a rika karramashi da kyaututtuka irin haka.
Portable ya ce ɗaure ya ƴan luwaɗi da maɗigo gindi ne haka ake yi.
Daga nan sai ya rangaɗa wa Bobirisky waka da a ciki ya rika caccakarsa ya na ce masa ” Yaya Allah zai halicce ka na miji amma kuma ka koma dole sai ka zama mace, wannan ai lalacewa mai lasisi.
Discussion about this post