An sanar da cewa gagarimin aikin gyaran wayoyin kebul na intanet da ke ƙarƙashin ruwan teku, wanda lalacewar su ya kawo matsalar intanet a Najeriya da wasu ƙasashen Afrika, zai iya kai makonni biyar ana faman gyara nan gaba.
Kamfanin MainOne, wanda shi ne ke samar da data wadda ake buɗe intanet da ita ƙasashen Afrika ta Yamma da ƙasashen Kudancin Afrika, shi ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.
A cikin sanarwar ta ranar Juma’a, MainOne ya kuma yi ƙarin bayani dangane da katsewar da wayoyin kebul ɗin suka yi a ƙarƙashin teku, sai kuma bayanin irin ƙoƙarin gyaran da ake kan yi.
Cikin sanarwar da kamfanin ya bayar a shafin sa na intanet, ya ce: “Wayoyin kebul ɗin intanet na MaiOne da ke ƙarƙashin teku su na kai saƙonni ƙasashen Afrika da dama shi ya sa hakan ta faru.”
MainOne ya ce sun rattaba yarjejeniyar gyara da kamfanin Atlantic Cable Maintenance and Repair Agreement (ACMA), domin ya gyara kebul ɗin can a ƙarƙashin ruwan teku.”
Sanarwar ta ce matakin farko shi ne a samu jirgin da zai yi ninƙaya a ƙarƙashin ruwa, domin ya gano ainihin wayoyin da suka katse, sai kuma gano daidai wuraren da za a yi gyaran.
Discussion about this post