Aƙalla mutum 61 aka tabbatar da an tasa ƙeyar su aka nausa da su cikin daji, yayin da ‘yan ta’adda suka afka wa ƙauyen Buda, wani gari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kajuru, a Jihar Kaduna, a ranar Litinin.
Mazauna garin sun shaida wa manema labarai cewa maharan sun afka wa garin ranar Litinin wajen 11:45 na dare.
Wani ɗan garin mai suna Dauda Kajuru, ya ce masu garkuwar sun dira ƙauyen suka riƙa harbi ta ko’ina.
“Abin da ya faru jiya Litinin abin firgici ne sosai. Maharan sun zo da yawan gaske. Sun zo da niyyar kwasar mutane da dama fiye ma da adadin 287 da suka jida a garin Kuriga, cikin makon da ya gabata. To amma zuwan da sojoji suka yi da wuri, tunda dama tsakanin mu da su bai fi kilomita 2 ba, sai ba a kwashi mutane fiye da 61 ba.
“An kwashi har da ƙanne na. Kuma labarin da muka ji a safiyar yau, har yanzu maharan na can na tafiya su na ƙara nausawa cikin surƙuƙin daji da su, ba su ƙarasa sansanin su ba.”
Mai bada labarin ya ce maharan sun yi abin da suka ga dama, ba wanda ya nemi hana su, saboda an ɗauke wani kwamandan sojoji da ke wurin, wanda ake wa laƙabi da Tega.
Ya ce a baya abin ya lafa, amma yanzu cire Tega da aka yi aka sauya masa wurin aiki ya sa ‘yan bindiga sun ci gaba da kai masu farmaki.
Wani mazaunin garin mai suna Lawal Abdullahi, wanda aka gudu da matar sa, ya tabbatar da cewa aƙalla mutum 61 aka gudu da su, ciki kuwa har da matar sa.
Ya ce daga cikin waɗanda abin ya ritsa da su, akwai mata, ƙananan yara har ma da wata maijego da ke shayarwa.
Har yanzu dai su ma ɗalibai 287 da aka gudu da su tun cikin makon da ya gabata, su na hannun ‘yan ta’adda.
Gwamnatin Jihar Kaduna dai zuwa yanzu ba ta ce komai dangane da harin ƙauyen Buda da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kajuru ba.
Lambar Kwamishinan Harkokin Tsaron Cikin Gida, Samuel Aruwan ba ta shiga ba, a ƙoƙarin kiran lambar da aka yi, domin jin ta bakin sa.
Shi na Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan na Jihar Kaduna, Mansir Hassan, an kasa samun sa.
Discussion about this post