Gwamnan Jihar Kaduna ya bayyana labari mai kwantar da hankali, na sako ɗaliban firamare da sakandare na garin Kuriga da ke hannun ‘yan ta’adda.
Ɗaliban dai sun shafe kwanaki 17 tun bayan arcewa da mahara suka yi da su daga makarantar su da sanyin safiya, a ranar 7 ga Maris, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun.
Tun a ranar Asabar da dare ne Gwamna Uba Sani ya yi wannan sanarwa.
“Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai, ina mai sanar da labarin ceto ɗaliban Kuriga.”
Sai dai Gwamna Uba Sani bai bayyana yadda aka sake su ɗin ba.
Kafin sakin su dai maharan sun nemi a biya fansar Naira biliyan 1 kafin su saki ɗaliban.
Amma kuma a bayanin da Gwamna Sani ya yi a ranar Asabar da dare, ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya ce shiga tsunduma wajen ƙoƙarin ganin an saki ɗaliban.
“Godiya ta musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, saboda maida hankali da ya yi wajen bada fifiko ga tsaron rayukan ‘yan Najeriya, musamman ganin an saki ɗaliban na Kuriga da aka yi garkuwa da su.
“Tun lokacin da ɗaliban ke hannun ‘yan ta’adda, na yi magana da Shugaban Ƙasa sau da dama, kuma ya jajanta tare da kwantar mana da hankula, kuma ya yi aiki wurjanjan wajen tabbatar da an dawo da yaran lami lafiya.
“Tilas kuma na yi godiya ya musamman ga ɗan’uwan mu Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman a Fannin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
“Ni da Ribadu mun sha hana idon mu barci muna tattauna yadda za a tsara dabarun da jami’an tsaron mu za su kuɓutar da ɗaliban. Kuma mun yi nasarar hakan.
“Su ma Sojojin Najeriya sun cancanci jinjina matuƙa, tilas a sara masu.
“Muna kuma godiya ga ɗimbin ‘yan Najeriya saboda addu’o’in da suka riƙa yi har yaran suka kuɓuta.”
Discussion about this post