Cutar Diphtheria ta yi ajalin yara hudu a ƙauyukan dake karamar hukumar Mingibir jihar Kano.
Jami’in Yaɗa Labarai na karamar hukumar Tasiu Yahaya ya sanar da haka ranar Alhamis a garin Kano.
“Cutar ta yi ajalin yara kanana hudu sannan wasu 28 sun kamu da cutar a kauyukan Kwarkiya, Kuru, Kunya da Minjibir dake karamar hukumar Minjibir.
Jami’in rikon kwarya na karamar hukumar, Muhammad Yakubu Kunya, ya yi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki da su gaggauta kaeo wa karamar hukumar Minjibir dauki domin dakile yaduwar cutar.
Hakimin Minjibir ya kuma bukaci sarakunan gargajiya da malaman addini da su tashi tsaye wajen wayar da kan mutane tare da yin addu’ar samun sauki.
A halin da ake ciki, ma’aikatar lafiya ta jihar ba ta tabbatar da bullowar cutar ba.
Sakamon binciken da Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ya nuna cewa jihar Kano ita ce jihar da ta fi fama da yaduwar cutar a kasar nan.
Sakamakon ya nuna cewa jihohin Kano, Yobe, Bauchi, Katsina da Borno na da kashi 98.9% daga cikin mutum 16,518 da suka kamu a Najeriya a 2024.
Menene cutar Diphtheria
Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa ta.
Cutar ya fi kama yara kananan da manyan musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cutar ba.
Hanyoyin kamuwa da cutar.
Ana iya kamuwa da cutar idan ana yawan zama kusa da masu fama da cutar.
Idan mai dauke da cutar ya Yi tari ko atishawa ba tare da ya rufe bakinsa ba.
Sannan da yawan yin amfani da kayan da masu ɗauke da cutar suka yi amfani da su kamar cokali, Kofi, hakichin da sauran su.
Mutanen da suka fi kamuwa da cutar
Cutar Diphtheria ya fi kama yara da manya musamman wadanda tun farko ba su Yi allurar rigakafin cutar suna yara ba sannan da kin yin allurar rigakafin yayin da suka girman.
Alamun cutar
Akan gane alamun cutar bayan ranar farko zuwa 10 da kamuwa da cutar.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da zazzabi, mura, ciwon makogwaro, idanun za su yi jajawur, tari da Kumburin wuya.
Wasu lokuta mai fama da cutar zai Rika ganin wasu farin abubuwa na fitowa da a kusa da makogwaron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi da hadiyan abinci.
Abin da ke haddasa cutar
Kwayoyin cutar ‘Corynebacterium diphtheria’ ne ke haddasa cutar inda yakan kama hanci, makogwaron da fatara mutum.
Discussion about this post