Zanga-zangar da mata suka gudanar a Minnna, babban birnin Jihar Neja dangane da tsadar kayan abinci da kuma tsadar rayuwa baki ɗaya, ta razana Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, lamarin da ya ƙara zaburar da shugaban bada umarni ga hukumomin da abin ya shafa su gaggauta daƙile hauhawar farashin kayan abinci a faɗin ƙasar nan.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka, bayan tashi daga taron da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Raba Agajin Abincin Gaggawa ya yi ranar Talata, a Abuja.
Idris ya ce Shugaban Ƙasa ya damu sosai dangane da yadda abinci ke ƙara tsadar nesanta kan sa daga talakawa a faɗin ƙasar nan.
“Gwamnati ta damu ƙwarai dangane da halin da ‘yan Najeriya ce fama yanzu, musamman abin da ya faru a Minna jiya Litinin,” cewar ministan, yayin da ya ke buga misali da zanga-zangar da mata suka fito a Minna, dangane da tsadar abinci.
“Kan haka ne gwamnati ta fara ɗaukar wasu matakai domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun samu sauƙi da rahusa, ta yadda abinci ba zai riƙa neman gagarar su ba.”
Ministan ya ƙara da cewa kwamitin zai ci gaba da yin taro har zuwa ranar Alhamis. Ya ce tuni har an fara ɗaukar wasu muhimman matakai, domin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar farashin kayan abinci.
“Daga cikin matakan akwai gaggauta fito da kayan abincin da gwamnatin tarayya ta tanadar a Rumbunan Ajiyar Abincin Gwamnati da ke faɗin ƙasar nan.
“Sannan kuma gwamnati na tattaunawa da manyan masu sarrafawa ko cashe kayan abinci da manyan ‘yan kasuwar kayan abinci da kayan masarufi, domin tantance adadin abin da suke da shi ajiye a runbunan ajiyar su.
“Dalilin yin hakan shi ne gwamnati na so ta gaggauta shiga cikin lamarin, domin abinci ya wadata ga ‘yan Najeriya.”
Sai dai kuma ya yi tsokacin cewa gwamnati na sane akwai wasu wasu marasa kishi kuma marasa tausayi da ke ɓoye abinci domin su sayar idan ya yi tsada sosai.
“Abin da zan shaida wa ‘yan Najeriya shi ne, Shugaban Ƙasa ya bada umarni cewa gwamnati ta gaggauta shiga cikin wannan lamari domin kawo sauƙi, ta hanyar daƙile masu ɓoye kayan abinci.
“Gwamnati ba za ta zura ido ‘yan Najeriya na fama da tsadar kayan abinci ba, alhali wasu na haifar da ƙarancin sa. Don haka ina roƙon jama’a su fahimci irin damuwar gwamnati da kuma ƙoƙarin da ta ke yi.
“Yayin da aka kammala waɗannan tarukan, za mu fito da sanarwa dangane da matsayi da matakan da gwamnati ta ɗauka.” Inji Idris.
Taron ya samu halartar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun da Mashawarcin Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu.
Sauran sun haɗa da Ministan Noma, Abubakar Kyari, na Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsare, Atiku Bagudu, sai kuma Ƙananan Ministocin Gona da FCT Abuja, Sabi Abdullahi da Mariya Mahmood.
Discussion about this post