Dakarun rundunar sojoji na ‘1Division’ dake Kaduna sun kashe ƴan bindiga 4 sannan da dama daga cikin sun gudu da raunin harsashi a jikinsu a arangama da suka yi da sojoji.
Mataimakin Shugaban hulda da jama’a na rundunar ‘1Division’ Musa Yahaya ya sanar da haka a wata sanarwa ranar Juma’a
Yahaya ya ce dakarun sun kama makamai da suka hada da AK 47 3, harsasai da babura biyu.
Yahaya ya ce dakarun sun fatattaki maharan a kauyen Kwaga dake jihar ranar Laraba bayan wasu sun zo sun sanar da su game da maharan.
“An yi batakashi tsakanin maharan da jami’an tsaron inda bayan sun fi karfin su maharan suka arce cikin daji.
Ya ce dakarun sun ceto mutum 11 da maharan suka yi garkuwa da su amma sai suka gudu suka barsu a dalilin arangamar da suka yi.
“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa maharan sun yi garkuwa da wadannan mutane ranar Talata a kauyen Masuku dake karamar hukumar Shiroro jihar Neja.
“Bayan likitoci sun duba lafiyar su ne aka hada kowa da ƴan uwan sa.
Ya ce kwamandan rundunar ‘1Division’ kuma kwamandan rundunar ‘Operation WHIRL PUNCH” Valentine Okoro ya yaba kokarin da dakarun suke yi na matsa kaimi wajen gamawa da ta’addanci sannan ya yi kira ga mutane da su ci gaba da mara wa jami’an tsaro baya domin ganin an kawo karshen wannan matsala a kasa baki ɗaya.
Okoro ya kara yin kira ga mutane da su gaggauta kai karar duk wanda suka gani da raunin harsashi a jikinsa ga rundunar tsaro.
Discussion about this post