Hukumar NDLEA reshen jihar Kaduna ta kama masu safarar muggan kwayoyi 92 sannan ta kama muggan kwayoyi masu nauyin kilogiram 217.02 daga watan Janairu zuwa farkon Faburairun 2024 a Kaduna.
Shugaban hukumar reshen jihar Kaduna Samaila Danmalam wanda ya sanar da haka a garin Kaduna ya ce daga cikin mutum 92 din da hukumar ta kama akwai maza 88 da mata hudu.
Danmalam ya ce hodar ibilis, tramadol, wiwi da methamphetamine na daga cikin kwayoyin da suka kama.
Ya ce hukumr ta samu nasarar kama mutane 24 da ake tuhuma tare da gurfanar da 25 a gaban kotu a lokacin.
“Mutum 7 daga cikin 29 din dake fama da matsalolin da ake kamuwa da su a dalilin ta’ammali da muggan kwayoyi sun warke.
“Hukumar ta kuma yi taro da akalla mutum 6,956 domin wayar da su illan dake tattare da shaye-shayen muggan kwayoyi.
Discussion about this post