Hukumar kula da ingancin magungunan da abinci ta kasa NAFDAC ta rufe wasu masan’antu uku dake sarrafa giyan leda a jihar Filato.
Jagoran ma’aikatan da suka rufe masana’antun a garin Jos Umar Suleiman ya ce hukumar ta rufe daya daga cikin masana’antun bisa laifin sarrafa giyan leda sannan da yin aiki ba tare da yin rajista da hukumar ba.
Suleiman ya ce sauran masana’antun an rufe su ne saboda rashin kiyaye sharuddan aiki da hukumar ta saka.
“Mun rufe masana’antun Bemag da Good Life Global Beverages saboda rashin kiyaye sharuddan aiki na NAFDAC sannan maasana’antar Stevenson Multi Global Ltd mun rufe shi ne saboda sarrafa giyan leda har na naira miliyan 6, rashin yin rajista da hukumar sannan da rashin kiyaye sharuddan aiyukan na hukumar.
Suleiman ya ce hukumar ta fara farautar masana’antun da ke sarrafa giyan leda tun bayan wa’adin da hukumar ta bada na hana sarrafa giyan leda a kasar nan da ya kare a ranar 31 ga Janairu.
Idan ba a manta ba a shekarar 2018 ne hukumar ta kafa dokar hana sarrafa giyan leda da wadanda ke cikin kwalaben 100ml, 20ml da 30 ml.
Suleiman ya ce hukumar ta kafa dokar ne domin hana ta’ammali da giya da mutane musamman matasa ke yi a kasar.
Ya ce tun a ranar 31 ga Janairu 2024 duk lasisin da masana’antu sarrafa giyan leda suka daina aiki a kasan.
Suleiman ya yi kira ga mutane da su guji siyan giyan leda da kayan da basu da rajista da hukumar domin da dama daga cikinsu na cutar da lafiyar mutum.
Discussion about this post